Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”
Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen ƙasar sun shanye saboda razana. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waɗansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
Sa'an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki.
Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”