Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki, Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce, “Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”
“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.
Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.