Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.
Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”
Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.