Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.
Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.
A sa'ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro. Yunusa ya ji kamar zai suma saboda zafin rana da take bugun kansa. Sai ya so ya mutu, ya ce, “Gara in mutu da ina zaune da rai.”