Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ga shi, zan datse abinci a Urushalima. Za su auna abincin da za su ci da tsoro, su kuma auna ruwan da za su sha da damuwa.
Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”
Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”