28 Ku dubi fuskata, Lalle ba zan faɗi ƙarya ba.
28 “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne?
Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce, Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
Bakina ba zai faɗi ƙarya ba, Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.
Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi. Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.
Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba, Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.
Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne? Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”