25 Kila muhawara mai ma'ana ta rinjaye ni, Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.
25 Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?
Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.
Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
Yana kuma fushi da abokan nan uku na Ayuba, domin sun rasa amsar da za su ba Ayuba, ko da yake sun hurta Ayuba ne yake da laifi.
Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne? Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”
“Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta'azantar da ni da maganganun banza. Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”
Kada ku faɗi kome, Wani sai ya ce kuna da hikima!
Idan wani ya yi tuntuɓe, Ya gaji, ya rasa ƙarfi, Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa, Har ya iya tsayawa kyam.
“To, sai ku koya mini, ku bayyana mini laifofina, Zan yi shiru in kasa kunne gare ku.
Kuna so ku amsa maganganuna? Don me? Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.
Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku, Me ya sa kuka zama wawaye?
Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!