12 Da dutse aka yi ni? Ko da tagulla aka yi jikina?
12 Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne?
Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse, Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.
Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.
Wane ƙarfi ne nake da shi na rayuwa? Wane sa zuciya kuma nake da ita, tun da na tabbata mutuwa zan yi?
Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina, Ba inda zan juya in nemi taimako.
“Kai ne mai taimakon marar ƙarfi, Kai ne mai ceton rarrauna!