6 Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa, Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.
6 Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa.
Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.
Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,
Zai yiwu mutane su rasa firgita, Idan aka busa ƙahon yaƙi a birni? Zai yiwu wata babbar masifa ta auko wa birni Ba da yardar Ubangiji ba?
Surutai kawai suke yi, Suna yin alkawaran ƙarya, Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.
Ba daga bakin Maɗaukaki Alheri da mugunta suke fitowa ne ba?
Mun halaka ta wurin fushinka, Mun razana saboda hasalarka.
Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi? Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa, Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?
Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”
Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi, Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara. Ai, ni ne na yi wannan.’
Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar.
Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta. Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”