Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.
Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.