Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala'ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”
Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!
Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.
Na sa masu duba su zama wawaye, Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari. Na bayyana kuskuren maganar masu hikima, Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
Sa'an nan Dawuda da mutanen da suke tare da shi, mutum wajen ɗari shida, suka tashi daga Kaila, suka tafi inda hali ya kai su. Da Saul ya ji Dawuda ya tsere daga Kaila, sai ya fasa tafiya can.
Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.