Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”
A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”
A zuciya ba su cewa, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.
Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.