Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 42:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na'ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Ayuba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 42:9
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta wurin bangaskiya Ibrahim ya yi biyayya, sa'ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasa da zai karɓa gādo. Ya kuwa fita, bai ma san inda za shi ba.


Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”


Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”


“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.


Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”


'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo, Su rusuna, su nuna bangirma. Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki. Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’ ‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’


Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.


Yanzu fa, sai ku kama bijimai bakwai da raguna bakwai, ku kai wa Ayuba, ku miƙa su hadaya ta ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi addu'a dominku, ni kuwa zan amsa addu'arsa don kada in sāka muku bisa ga wautarku. Gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.”


Sa'ad da ka yi addu'a zai amsa maka, Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.


Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.


Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa'ad da ya yi addu'a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da riɓin abin da yake da shi dā.


ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.


Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.


Zai ceci wanda yake da laifi, Idan abin da kake yi daidai ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ