Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.
Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.
“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.
“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.
Gama na tuba saboda na rabu da kai, Bayan da aka ganar da ni, sai na sunkuyar da kai, Kunya ta kama ni, na gigice, Domin ina ɗauke da wulakancin ƙuruciyata.’
Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji?
“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.
Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.