Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
Ya Ubangiji, na ji labarinka, Sai tsoro ya kama ni. Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu, Ayyukan da ka saba yi. Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.