9 Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi, Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.
9 Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.
Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al'amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama.
Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!
Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Zan yi wa Isra'ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana.
Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata.
In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!
Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi. Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?