Suka taurare zuciyarsu kamar dutse don kada su ji dokoki da maganar da ni Ubangiji Mai Runduna na aiko ta wurin Ruhuna zuwa ga annabawa na dā. Domin haka ni Ubangiji Mai Runduna na aukar musu da hasala mai zafi.
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.