21 Numfashinsa yakan kunna gawayi, Harshen wuta yana fita daga bakinsa.
21 Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta.
Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa, Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.
Annoba tana tafe a gabansa, Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.
An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.
Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko Daga cikin walƙiya da take gabansa, Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.
Hayaƙi na fita daga hancinsa Kamar tururi daga tukunya mai tafasa, Ko bāgar da ta kama wuta.
A wuyansa ƙarfi yake zaune, Razana tana rausaya a gabansa.
Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu. Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!