2 Ka iya sa wa hancinsa asirka? Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya?
2 Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?
Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”
A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.
Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”
Zai ta yi maka godo? Zai yi maka magana da tattausar murya?
Allah mai hikima ne, mai iko, Ba wanda zai iya ja in ja da shi.
Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.