15 An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne, An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.
15 An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai.
Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”
Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.
Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.
Wa zai iya buɗe leɓunansa? Gama haƙoransa masu bantsoro ne.
Suna haɗe da juna gam, Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.