“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.
Raina yana tsakiyar zakoki, Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane. Haƙoransu kamar māsu da kibau suke, Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.