Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 40:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka? Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 40:2
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.


Da wa Allah yake yin shawara Domin ya sani, ya kuma fahimta, Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?


Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni, Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?


Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni,


Gama Allah yana kusa, Zai tabbatar da ni, marar laifi ne, Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari'a tare! Bari ya kawo ƙararrakinsa!


“Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami, Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?


“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.


Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi? Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.


Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba, Ya kalmashe su kowane gefe.


“Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa? Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?


Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?


Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba.


Ka zama mugu a gare ni, Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.


“Ya Ubangiji, don me ka sa ni a waƙafi? Kana tsammani ni dodon ruwa ne?


Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.


Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba, Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.


Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.


“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,


Na kafa miki tarko, ya kuwa kama ki, ya Babila, Ke kuwa ba ki sani ba. An same ki, an kama, Domin kin yi gāba da ni.”


Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ