Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu, Nesa da gidajensu.
Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a gidana?” Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman.