Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”
Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”
“Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.
Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa, Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo. Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta, Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba, Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.
Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.