9 A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.
9 A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.
Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba. Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa, Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.
An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.
Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu.
Saboda haka, sai ka tuba. In ba haka ba kuwa, zan zo a gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da yake a bakina.
Kashiyar teku ta bayyana, Tussan duniya sun bayyana, Sa'ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji, Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.
Dukansu ka binne su a ƙasa, Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.
sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe 'ya'yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”
Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.
Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru, Rigyawa ta tsaya kamar tudu, Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.
Ka kwararar da rigyawar fushinka, Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.
Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu. Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!