5 Yanzu naka lokacin wahala ya zo, Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
5 Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.
Ku abokaina ne! Ku ji tausayina! Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.
Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato “Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji, Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.
Ku fa, dubi wannan da ya jure irin gābar nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai.
Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.
Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.
Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.
“A cikin irin wannan wahala Ina bukatar amintattun abokai, Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.
Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”
Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”
Idan wani ya yi tuntuɓe, Ya gaji, ya rasa ƙarfi, Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa, Har ya iya tsayawa kyam.
Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Ina roƙon taimakonka.