“Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.
Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.
Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.