12 “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali, Har da ƙyar nake iya ji,
12 “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.
Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al'amuransa. Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa. Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?”
Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.
Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.
Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi Sa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su, A sa'ad da suke barci a gadajensu.
Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa, Na gane da shi sarai. Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani. Ba ku fi ni da kome ba.