Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
Kamar jakar jeji kake, wadda take son barbara, Wadda take busar iska, Sa'ad da take son barbara, wa zai iya hana ta? Jakin da take sonta, ba ya bukatar wahalar da kansa Gama a watan barbararta za a same ta.
Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.
Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.”