23 Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa.
23 Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba. Ba ya ba da baya ga takobi,
Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa, Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.
Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, Sojojinsa kuma suna saye da mulufi. Da ya shirya tafiya, Karusai suna walƙiya kamar harshen wuta, Ana kaɗa mashi da bantsoro.