22 Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba. Ba ya ba da baya ga takobi,
22 Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
A duniya ba kamarsa, Taliki ne wanda ba shi da tsoro.
Amma sa'ad da ta sheƙa a guje, Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.
Takan yi wa 'ya'yanta mugunta, Sai ka ce ba nata ba ne, Ko da yake ta sha wahala a banza, Duk da haka ba ta damu ba.
Yakan yi nishi a fadama, Yana murna saboda ƙarfinsa, A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.
Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa.
Ku ji amon bulala da kwaramniyar ƙafafu, Da sukuwar doki da girgizar karusai!