2 Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin haihuwarsu?
2 Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa?
Kamar jakar jeji kake, wadda take son barbara, Wadda take busar iska, Sa'ad da take son barbara, wa zai iya hana ta? Jakin da take sonta, ba ya bukatar wahalar da kansa Gama a watan barbararta za a same ta.
“Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa? Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu, Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu?