Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”
Ba sauran iri a rumbu. Kurangar inabi kuma, da itacen ɓaure, da rumman, da itacen zaitun ba su ba da amfani ba tukuna. Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ”
A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.