9 Sa'ad da na suturta ta da gizagizai, Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.
9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.
“Wa ya yi wa teku iyaka Sa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?
Na sa mata iyakoki, Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,
Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!