Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.
Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!
Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?