Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?
Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta, Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama, Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar 'yan ƙananan ƙwari. Ya miƙa sararin sama kamar labule, Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.
Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.
Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.