Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!
Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.
Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!