Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.