Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara, Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri, Shi ne yake bai wa mutane yayyafi. Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.
Ubangiji ne ya yi taurarin Kaza da 'ya'yanta Da mai farauta da kare. Ya mai da duhu haske, Rana kuwa dare. Shi ya kirawo ruwan teku ya bayyana, Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa. Sunansa Ubangiji ne.
Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai.