30 Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse, Teku ta daskare.
30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?
Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara, Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.
Wace ce mahaifiyar ƙanƙara? Wace ce kuma ta haifi jaura?
“Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta? Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?
Idan yana wucewa sai a ga hasken dārewar ruwa, Yakansa zurfafa su yi kumfa.