A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”
domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.
Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.
Ya ku mutanen Sihiyona, ku yi murna, Ku yi farin ciki da Ubangiji Allahnku, Gama ya ba ku ruwan farko Domin shaidar gafarar da ya yi muku, Ya kwararo muku da ruwan farko da na ƙarshe da yawa kamar dā.
Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.
A zuciya ba su cewa, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
“Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa. Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani. Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance, Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.