27 Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa, Har ta tsiro da ciyayi?
27 don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?
Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa, Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.
Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu, Tsire-tsire kuma don amfanin mutum, Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,
Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya, Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.
Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba, Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu, Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.
Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi. Ya tanada wa duniya ruwan sama, Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.