Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.
Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala'in ƙanƙarar. Bala'in nan da matuƙar bantsoro yake!
Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma.