Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!
Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.
Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.