Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa.
Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.
Da Suriyawa suka gangaro wurinsa, sai Elisha ya yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ka bugi mutanen nan da makanta.” Ubangiji kuwa ya buge su da makanta bisa ga addu'ar Elisha.