14 Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi, Yakan rine kamar riga.
14 Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.
Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba, Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
Ka yi lulluɓi da haske. Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.
Da gari ya waye, Ka kawar da muguntar da ake yi da dare?
Akan hana wa mugaye haske, Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.