Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku.
Ubangiji ne ya yi taurarin Kaza da 'ya'yanta Da mai farauta da kare. Ya mai da duhu haske, Rana kuwa dare. Shi ya kirawo ruwan teku ya bayyana, Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa. Sunansa Ubangiji ne.