Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 38:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan, Ba za ki wuce ba. Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 38:11
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kai kake mulkin haukan teku, Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.


Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa. Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya.


Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.


Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Ko da yake waɗannan al'amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.


Na sa mata iyakoki, Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,


“Ayuba, a dukan kwanakinka Ka taɓa umartar wayewar gari, Ko ka sa alfijir ya keto?


Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba, Don kada ya sāke rufe duniya.


ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.


Ya shata da'ira a kan fuskar teku, A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.


Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ