Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.
Ubangiji mai jinkirin fushi ne, Mai Iko Dukka. Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin hadiri, Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.
Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.