9 Guguwa takan taso daga inda take, Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.
9 Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
Allah ya rataye taurari a sararin sama, Wato su mafarauci da kare da zomo, Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu.
Wannan shi ne jawabi a kan Babila. Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.
Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama. Gajimare ne karusanka, A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su, Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya, Ubangiji Allah zai busa ƙaho, Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.
Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.
Yakan aiko da ƙanƙara kamar duwatsu, Ba wanda yake iya jurewa da sanyin da yakan aiko!
Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.